Limamin Juma'ar Birnin Tehran Ya Bukaci Hadin Kan Al'ummar Iran
Limamin da ya jagoranci sallar juma'a a nan birnin Tehran ya bayyana cewa ya kamata a dukkanin matakan gudanar da zaben Shugaban kasa a kiyaye hadin kan Al'umma kasa da kuma ka'idojin Siyasa.
Ayatollah Muhamad Imami Kashani cikin Khudubar Juma'ar da ya gabatar a yau Juma'a ya bayyana cewa shakka babu batun zaben Shugaban kasar Iran nada mahimanci, to amma abinda ya fi mahimanci shi ne kiyaye hadin kan Al'ummar kasa, domin shekaru 38 da suka gabata, Al'ummar nan ta kwashe tana sadaukar da kai wajen bayar da goyon baya ga juyin juya halin musulinci wanda kuma hakan shi ya kawo ci gaban da kasar take da shi a yau.
Yayin da yake ishara a kan shirin makiya na kutse da kuma gurgunta juyin juya halin musulinci, Ayatollah imami Kashani ya ce bai kamata 'yan takarar Shugabancin kasar da magoya bayan su su dinga firta kalaman da su dauke nutsuwar da Al'umma ke da ita dangane da tsarin musulinci.
Har ila yau Ayatollahi Imami ya bukaci 'yan takarar Shugabanci da su kiyaye hadin Al'ummar kasar cikin ko wani hali tare kuma da dakile duk wani kutse da Maƙarƙashiyar makiya domin illata tsarin musulinci na Iran.
A ranar 19 ga watan Mayun nan da muke ciki ne za a gudanar da zaben Shugabanci kasar ta Iran.