Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Kada Kuri'arsa
Da kimanin karfe 8:00 agogon kasar Iran ne jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya kada kuri'arsa a zaben shugaban kasa da kuma na kananan hukumomi da ake gudanarwa yau a kasar.
Jim kadan bayan kada kuri'ar tasa a husainiyyar Imam Khomenei a birnin Tehran, jagoran ya yi dan gajen jawabi wanda aka watsa kai tsaye a dukkanin kafofin yada labarai na kasar Iran.
Jagoran ya kirayi dukkanin al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri'unsu a wannan zabe, tare da bayyana muhimamncin hakan ga makomar kasa.
Kamar yadda ya mika godiyarsa ga dukkanin bangarori da suke gudanar da ayyuka domin ganin komai ya tafi yadda ya kamata a wadannan zabuka, musamman ma'aikatan hukumar radiyo da talabijin na kasar da suke nuna hakikanin abin da yake faruwa kai tsaye a dukkanin wuraren zabukan.
Daga karshe ya yi fatan alkhairi ga dukkanin al'ummar kasar da sauran musulmi na duniya.