Shugaba Rauhani Ya Gana Da Fira Ministan Iraki A Tehran
Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani ya gana da Fira ministan kasar Iraki Haidar Abadi a birnin Tehran, a ziyarar aiki da Fira ministan na Iraki ke gudanarwa a kasar Iran.
A yayin ganawar tasu shugaba Rauhani ya taya Haidar Abadi murnar nasarar da dakarun Iraki suka samu wajen karya lagon 'yan ta'adda a kasar, tare da bayyana wannan nasara ta dakarun Iraki da cewa nasara ce da dukkanin al'ummomin yankin gabas ta tsakiya suke murna da ita.
Rauhani ya jaddada goyon bayan Iran ga kudirin gwamnatin Iraki na ci gaba da zaman Iraki a matsayin kasa guda da al'umma guda, duk da banbancin addinai da mazhabobi da kuma kabilu.
A nasa bangaren Haidar Abadi ya yaba da irin goyon bayan da Iran take baiwa Irakia dukkanin bangarori na siyasa, tattalin arziki da kuma tsaro, tare da jaddada cewa kasashen biyu masu tsohuwar alaka ta tarihi na dubban shekaru, za su ci gaba da kasancewa tare da juna.