Iran Ta Aike Da Sakon Ta'aziyya Da Alhini Ga Gwamnatin Kasar Pakistan
(last modified Sun, 25 Jun 2017 12:23:42 GMT )
Jun 25, 2017 12:23 UTC
  • Iran Ta Aike Da Sakon Ta'aziyya Da Alhini Ga Gwamnatin Kasar Pakistan

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aike da sakon ta'aziyya ga gwamnatin Pakistan da al'ummar kasar kan hasarar rayukan da suka yi sakamakon fashewar wata tankar man fetur a kasar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahroum Qasimi ya sanar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aike da sakon ta'aziyya da alhini ga gwamnatin Pakistan da al'ummar kasar kan irin hasarar rayukan da suka yi sakamakon fashewar wata motar dakon man fetur a kasar.

A safiyar yau Lahadi ce wata motar dakon man fetur ta fadi a garin Bahawalpur da ke lardin Poinjab na kasar Pakistan, inda man da take dauke da shi yake zuba, ganin haka jama'a suka zo kwasar bati, inda daga bisani tankar man ta tarwatse lamarin da ya janyo hasarar rayukan mutane akalla 123 yayin da wasu fiye da 80 suka samu raunuka.