Mafi Yawan Mambobin Kwamitin Tsaro Sun Amince Da Shirin Iran Na Nukiliya
Rahoto na uku wanda babban sakataren majalisar dinkin duniya ya gabatarwa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan shirin Nukliyar kasar Iran a cikin yerjejeniyar tsakanin kasashe 5+1, wanda kuma yake kunshe cikin kudirin kwamitin tsaron na 1231 ya nuna cewa Iran tana rike da alkawarinta .
Antonio Gutarosh ya fadawa kwamitin tsaron cewa bisa rahotanni guda 7 da ya karba daga hukumar IAEA wacce kwamitin tsaron ya dorawa nauyin sanya ido a kan shirin Nukliyar Iran da kuma yadda take kiyaye yarjejeniyar da ta cimma da manya -anyan kasashen duniya, sun nuna cewa kasar Iran tana rike da alkawarinta.
Bayan wannan rahoton dai mafi yawan wakilan kwamitin tsaron da kuma wakiliyar kungiyar tarayyar Turai duk sun amince da cewa iran tana ciki alkawarin da ta dauka. Sai dai babban sakataren ya yi kira ga kasar Iran da ta nisanci cilla makaman linzami na bilistic, amma ba don yana daga cikin yarjejeniyar da ta cimma da manya manyan kasashen duniya kan shirinta na makamashin nukliaya ba.
Amma wakiliyar gwamnatin Amurka a kwaitin tsaron ta dake kan cewa cilla makaman linzami wanda gwamnatin kasar Iran take yi ya sabawa kuduri na 2231 kan shirinta na makamashin nukliya. Har'ula yau wakilyar Amurka a komitin tsaron ta bayyana Iran gwaje- gwajen makamai da Iran take yi da kuma masu bada shawara kan harkokin tsaro da take aikawa zuwa kasar siria su suka hana samar da tabbataccen zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
Kwamotin tsaron ya kawo karshen zamansa a ranar Alhamis da ta gabata ba tare da sauya matsayinsa kan yerjejeniyar ba duk tare da babatun da Amurka ta yi ta yi don ganin kwamitin ya sauya matsayi dangane da yarjejeniyar.
Kafin haka dai a makonnin da suka gabata ne, majalisar dattawan kasar Amurka ta amince da wasu sabbin takunkumai kan kasar Iran da sunan ta sabawa yarjejeniyar ta Nukliya.
A karshen zaman komitin a ranar Alhamis ta ta gabata wakilin kasar rasha a kwamitin tsarin ya zargi kasar Amurka da kuma babban sakataren majalisar dinkin duniya kan kawo batun shirin makaman linzami na kasar Iran da kuam rikicin gabs ta tsakiya a rahotannin da suka gabatar a zaman. Wakilin na Rasha ya bayyana cewa shirin makaman linzamin kasar Iran da kuma rawan da irin take takawa a rikicn gabas ta tsakiya ba su da dangantaka da kudurin kwamitin tsaron na 2231.
Don haka wannan karon ma kasar Amurka ta kasa cimma burinta na ganin bayan yarjejeniyar shirin makamashin Nukiliya tsakanin Iran da kasashe 5-1 suka cimma a shekara ta 2015M.
Sabuwar gwamnatin Amurka dai tana ganin cewa babban kuskure ne gwamnatin Amurka da ta shude ta tabka wajen amincewa da yarjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran.