Kasashen Iran Da Uganda Na Fatan Kara Karfafa Hulda Tsakaninsu
Jadakan Jamhuriya Musulinci ta Iran a Uganda ya gana da mukadanshin Firayi Ministan kasar, inda bangarorin biyu suka sanar da wajabcin kara hulda a tsakaninsu.
Jami'in diflomatsiya na Iran ya ce yana da kyawo bangarorin biyu su yi hulda ta fuskar tattalin arziki, masana'antu, da noma musamen ma bayan yarjejeniyar nukuliyar data kai ga yayewa Iran din kallabin takunkumin kasa da kasa.
A daya banagaren kuwa jakdan na Iran ya mika goron gayyata ga hukumomin na Uganda akan halartar bikin rantsarda shugaban kasar Hassan Rohani da za'a yi a ranar 5 ga watan gobe.
Mataimakin firayi ministan na Uganda ya yaba da wannan gayyata wancce ya danganta da wata dama ta sake ziyartar Iran.
A hannun daya kuma jakadan na Iran ya dauko batun halin da ake ciki a gabas ta tsakiya, inda ya jaddada wajabcin hadin gwiwa don yaki da ta'addanci da kuma hadin kai na kasashen musulmi.