Iran Ta Kafa Kwamitin Sa Ido A Kan Yarjejeniyar Nukiliya
Gwamnatin Iran ta kafa wani kwamiti a jiya, wanda zai sanya ido a kan yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, gami da kungiyar tarayyar turai.
A zaman da majalisar ministocin kasar Iran ta gudanar a jiya, an kafa wannan kwamiti a karkashin jagorancin shugaba Hassan Rauhani, domin yin dubi a kan wannan yarjejeniya, da kuma daukar dukkanin matakan da suka dace a kan batun.
Kungiyar tarayyar turai ta sanar da cewa za ta ci gaba da yin aiki da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimmawa tare da Iran, kamar yadda majalisar dinkin duniya da kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya suka sanar da irin wannan mataki, amma Amurka karkashin shugabancin Trump, tana kai komo domin ganin ta rusa wannan yarjejeniya, lamarin da sauran bangarorin duniya suka ki bata hadin kai a kansa.