Bikin Rantsar Da Shugaba Rauhani Na Iran A Wa'adin Shugabanci Na Biyu
(last modified Sat, 05 Aug 2017 05:56:30 GMT )
Aug 05, 2017 05:56 UTC
  • Bikin Rantsar Da Shugaba Rauhani Na Iran A Wa'adin Shugabanci Na Biyu

A yau ne shugaban kasar Iran Hassan Rauhani zai yi rantsuwar kama aiki a wani sabon wa'adin shugabancin kasar Iran na biyu, bayan da aka gudanar da taron tabbatar da shi daga bangaren jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei a ranar Alhamis da ta gabata.

Tun a jiya ne tawagogi daga kasashen duniya suke ci gaba da isowa birnin Tehran domin halartar taron rantsar da shugaba Rauhani, inda ake sa ran tawagogi daga kasashe 92 ne za su halarci taron na yau, da suka hada da shugabannin kasashe, da kuma mataimakan shugabanni da kuma shugabannin gwamnatoci gami da shugabannin majalisu da kuma ministoci gami da wakilai na musamman daga kasashe da kuma kungiyoyi na kasa da kasa da sauransu.

Tun a jiya ne dai shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, da kuma sarkin Lesotho Letsie na uku da Muhammadu Bawumia mataimakin shugaban kasar Ghana suka iso birnin Tehran, kamar yadda wasu tagawagogin jami'ai da wakilai daga kasahe daban-daban na Afirka , da suka hada Senegal, J. Nijar, Najeriya da sauransu suke ci gaba da isowa.

A bangaren kasashen nahiyar turai kuwa babbar jami'a mai kula harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini da ke jagorantar tawagar kungiyar tarayyar turai sun iso birnin Tehran a daren jiya, kamar yadda wakilai da suka hada da ministoci da shugabannin majalisu daga kasashe 23 na nahiyar turai za su halrci taron daga bangaren gwamnatocinsu, haka nan kuma daga kasashen Asia da Latin Amurka da gabas ta tsakiya, shugabannin kasashe da sarakuna da kuma ministoci gami da shugabannin majalisun dokoki daga kasashe daban-daban ne suke ci gaba da isowa birnin Tehran domin halrtar wannan taro na rantsar da shugaba Rauhani da za a gudanar a yau.

A lokacin da ya gabatar da jawabinsa a ranar Alhamis da ta gabata a wurin taron tabbatar da shi, Dr. Rauhani ya bayyana cewa, Iran za ta ci gaba da kyautata alakarta da dukkanin kasashen duniya, a bangarori na siyasa, tattalin arziki, tsaro, al'adu da dai sauransu, duk kuwa da irin da matakan da sabuwar gwamnatin Amurka take dauka na kokarin ganin ta mayar da Iran saniyar ware, wanda ya ce hakan ba zai nasara ba.

Haka na  kuma a bangaren ayyukan da zai mayar da hankali a kansu, Rauhani ya bayyana cewa, gudanar da ayyukan ci gaban kasa da bunkasa ilimi a dukaknin fagage na kimiyya da fasaha da kere-kere da karfafa kamfanoni da masana'antu na cikin gida domin samar da guraben ayyukan yi ga matasa musamman, na daga cikin abubuwan da zai kara mayar da hankali a kansu.

Haka nan kuma Rauhani ya bayyana cewa, a daidai lokacin da gwamnatinsa take karfafa ayyukan dogaro da kai na cikin gida, kofa bude take ga gwamnatoci ko daidaikun 'yan kasuwa ko kamfanoni masu saka hannayen jari na kasashen ketare a bangarorin daban-daban da za su iya yin aiki tare da Iran.

Wannan dai shi ne karo na 12 da zababben shugaban kasa zai sha rantsuwar kama aiki a wa'adin shugabanci a kasar Iran, tun bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar a cikin shekara ta 1979 a karkashin jagorancin marigayi Imam Khomeini,  kuma tun daga lokacin ne kasar ta koma tana cin gashin kanta ta fuskar siyasa da tattalin arziki, tare da ficewa daga cikin kasashe masu mika wuya ga manufofin 'yan mulkin mallaka, wanda hakan ne yasa manyan kasashen duniya musamman Amurka da sauran tsoffin 'yan mulkin mallaka, suka shiga takun saka da ita, tare da kakaba mata takunkumai da haifar mata da matsaloli a dukkanin bangarori na siyasa da tattalin arziki da sauransu, yayin da kasar ta Iran ta yi amfani da hakan a matsayin damar karfafa kanta, wanda hakan ya bata damar samun ci gaba a dukkanin fagage na ilimi da fasahar kere-kere da kuma ta fuskar soji.