Zarif: Babu Ruwan Musulunci Da Ayyukan Ta'addanci Da Ake Yi Da Sunansa
(last modified Sat, 19 Aug 2017 16:36:02 GMT )
Aug 19, 2017 16:36 UTC
  • Zarif: Babu Ruwan Musulunci Da Ayyukan Ta'addanci Da Ake Yi Da Sunansa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar babu ruwan Musulunci da ayyukan ta'addancin da ake aikatawa da sunansa.

Ministan harkokin wajen na Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump wanda ya 'zargi' Musulunci sakamakon harin ta'addancin da aka kai kasar Spain a shekaran jiya, inda ya ce ayyukan ta'addancin da aka aikata da sunan Musulunci, ko da wasa ba sa wakiltan addinin Musulunci.

Dakta Zarif ya bayyana mamakinsa kan yadda shugaban Amurka yayi gaggawan zargin Musulunci amma ya gaza wajen yin Allah wadai da hare-haren nuna wariyar launin fata da ke faruwa a Amurkan.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai ta yi Allah wadai da wadannan hare-hare da aka kai kasar Spain din a shekaran jiya tana mai bayyana cewar Musulunci yayi hannun riga da duk wani aikin ta'addanci.