Iran Za Ta Ci Gaba Da Goyon Baya Da Karfafa Kungiyoyin Gwagwarmaya
(last modified Sun, 03 Sep 2017 10:51:23 GMT )
Sep 03, 2017 10:51 UTC
  • Iran Za Ta Ci Gaba Da Goyon Baya Da Karfafa Kungiyoyin Gwagwarmaya

Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Amir Hatami ya bayyana cewa Iran za ta ci gaba da goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya duk kuwa da kokarin da kasashen yammaci suke yi wajen ganin Iran ta daina goyon bayansu musamman kungiyar Hizbullah.

Janar Amir Hatami, ministan tsaron na Iran, ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da tashar talabijin din Al-Alam da ke watsa shirye-shiryenta da harshen larabci daga nan Tehran inda ya ce gwagwarmaya wani lamari ne da sami gindin zama cikin ala'adun Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Janar Hatami ya kara da cewa gwagwarmaya tana nufin tsayin daka wajen tinkarar ma'abota girman kai da sauran azzalumai, don haka goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya wani lamari ne da  ke cikin koyarwar addinin Musulunci wanda shi ne tushen tsarin kasar Iran. Don haka ya ce ko shakka babu Iran za ta ci gaba da goyon bayan wadannan kungiyoyi.

Cikin shekarun nan dai Amurka da kawayenta suna ci gaba da matsin lamba wa Iran sakamakon goyon bayan da take ba wa kungiyoyin gwagwarmaya wadanda suke fada da bakar siyasar ma'abota girman kai da 'yan amshin shatansu irin kungiyoyin 'yan ta'addan takfiriyya da suka kirkiro da nufin bata sunan Musulunci.