Iran : An Yi Jana'izar Shahid Hujaji
(last modified Thu, 28 Sep 2017 11:18:09 GMT )
Sep 28, 2017 11:18 UTC
  • Iran : An Yi Jana'izar Shahid Hujaji

A yau ne dubun dubatan mutanen garin Najafabad da ke nan Iran ne suka gudanar da jana'izar Shahid Muhsin Hujaji, daya daga cikin dakarun kasar Iran da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh suka kama da yanka shi a kasar Siriya, inda aka bisne shi da garin haihuwarsa na Najafabad.

Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya ce tun da safiyar yau Alhamis ne dai dubun dubutan al'ummar garin Najafabad din cikin yanayi na juyayi sanye da bakaken kaya suka fito kan titunan garin don maraba da shahidin da yi masa rakiya zuwa makwancinsa na karshe.

Rahotanni sun bayyana cewar garin na Najafabad dai ya cika da manyan jami'an soji da na siyasa na Iran, wadanda suka hada da Manjo Janar Husain Salami, mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran wadanda suka iso garin na Najafabad don halartar jana'izar Shahid Muhsin Hujaji, inda bayan sa'oi na jana'izar aka yi masa salla da kuma bisne shi.

A jiya ne dai aka iso da gawar tasa daga birnin Mashad zuwa birnin Tehran inda daga cikin wadanda suka halarci wajen da aka ajiye gawar har da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da sauran manyan jami'an gwamnati.

A kwanakin baya ne dai 'yan kungiyar ta'addancin nan na Da'esh suka kama shahid Muhsin Hujaji a kasar Siriya inda ya tafi can din don ba da kariya ga wajaje masu tsarki na Musulunci da suke wajen daga hareharen 'yan Da'esh din suke son rusa, inda suka masa yankan rago bayan azabtarwar da suka yi masa.