Ministan Tsaron Iran Ya Gargadi Trump Kan Sanya IRGC Cikin Kungiyoyin Ta'addanci
(last modified Thu, 12 Oct 2017 17:23:25 GMT )
Oct 12, 2017 17:23 UTC
  • Ministan Tsaron Iran Ya Gargadi Trump Kan Sanya IRGC Cikin Kungiyoyin Ta'addanci

Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Amir Hatami ya jan kunnen shugaban Amurka Donald Trump dangane da sanya dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran (IRGC) cikin kungiyoyin 'yan ta'adda yana mai cewa yin hakan ba abin da zai haifar in ban da kara zaman dardar da kuma yaduwar ta'addanci a yankin Gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.

Birgediya Janar Amir Hatami, Ministan tsaron na Iran, ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da yake mayar da martani ga barazanar ta Trump inda ya ce dakarun IRGC din dai suna daga cikin dakarun da suke sahun gaba wajen fada da ta'addanci, don haka duk wani kokari na bata sunansu ba abin da zai haifar face taimakon yaduwar ayyukan ta'addanci.

Har ila yau ministan tsaron na Iran ya sake jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na fuskantar duk wata barazanar Amurka, yana mai cewa dakarun kare juyin, sojoji da sauran dakarun kasar Iran bakinsu ya zo daya wajen tsayin daka da kuma tinkarar barazana da girman kan Amurka.

A ranar 15 ga watan Oktoban nan ne dai ake sa ran Shugaban Amurkan zai sanar da wasu siyasar gwamnatinsa kan Iran musamman kan yarjejeniyar nukiliya da kuma dakarun kare juyin juya halin Musulunci, lamarin da jami'an Iran suka ce suna nan suna zuba ido kuma za su mayar wa Amurkan da martanin da ya dace.