Oct 14, 2017 18:29 UTC
  • Ganawar Sashen Hausa Tehran Da Jakadan Najeriya A Iran Alh. Hamza Ibrahim Tsiga

A yau 14 ga watan Oktoban 2017, jakadan tarayyar Najeriya a Iran Alh. Hamza Ibrahim Tsiga ya mika takardunsa na kama aiki a hukumance ga shugaba Rauhani.

Jim kadan bayan ganawarsa da shugaba Rauhani, Sashen Hausa na muryar Jamhuriyar muslunci ta Iran ya zanta da shi dangane da ganawar tasa tare da shugaba Rauhani da ma wasu batutuwa na daban da suka shafi aikinsa.

Jakadan na Najeriya a Iran ya bayyana farin cikinsa dangane da yadda ganawar tasa ta kasance a yau tare da shugaba Rauhani, inda ya ce shugaba Rauhani ya tabbatar masa da cewa Iran a shirye take ta kara fadada alakarta da tarayyar Najerya a dukkanin bangarori, domin ci gaban kasashen da kuma amfanin al'ummominsu, wadanda suke da hulda da alaka ta tsawon shekaru masu yawa.

A lokacin da yake amsa tambaya kan yadda ya ga yanayin kasar ta Iran da kuma yiwuwar ko za a samu nasara kan abin da aka sanya  a gaba, Jakadan Najeriya ya bayyan cewa hakika akwai dama da ya kamata Najeriya ta yi amfani da ita ta yadda dukkanin bangarorin biyu za su ci moriyar juna, musamman a bangarori na ci gaban ilimi, da kuma kasuwanci da sauran harkokin na habbaka tattalin arziki, inda ya ce hatta 'yan kasuwa daga Najeriya za su iya amfana da wannan damar, maimakon dogaro da kashen turai a mafi yawan lokuta.

Ya bayyana muhimman abubuwan da zai mayar da hankali a kansu a halin yanzu, da suka hada batun ayyukan noma, wanda a halin yanzu yana daga cikin muhimman abubuwa da Najeriya ta mayar da hankali a kansu, wanda kuma a cewarsa Iran tana da tsare-tsare na zamani da dama ta fuskar noma, wanda za su iya yin aiki tare da Najeriya a wannan bangare, haka nan batun karfin wutar lantarki, wanda Iran tana samar da Megawatt fiye da 70,000 a halin yanzu, yayin da Najeriya take samar da wajen 7000.

Haka nan kuma ya bayyana jin dadinsa dangane da irin abin da ya kira da kyakkyawar tarba da ya samu a kasar, daga bangaren mahukunta da kuma sauran jama'a da yake yin mu'amala da su.

Dangane da dalibai 'yan Najeriya da suke karatu a jami'oi daban-daban na Iran, wadanda adadinsu ya kai daruruwa, ya bayyana jin dadinsa kan hakan, tare da shan alwashin bin kadun dukkanin lamurra da suka shafi 'yan Najeriya da suke zaune a kasar ta Iran, da kuma jin korafe-korafensu da kuma daukar matakai na taimaka musu a  bangarorin da suke bukatar taimakon ofishin jakadancin Najeriya.

Dangane da aiwatar da yarjeniyoyin da aka cimmawa  a baya da kuma wadanda za a cimmawa a nan gaba tsakanin Najeriya da Iran, jakakada Alh. Hamza Ibrahim Tsiga ya bayyana cewa, yanzu haka akwai kamfanonin Iran da dama da suke da shirin zuwa Najeriya domin gudanar da ayyuka a bangarori daban-daban, kamar yadda kuma wasu daga cikin manyan asibitocin kasar suka nuna sha'awarsu ta bude rassa a Najeriya, kasantuwar Najeriya kasa ce mai matukar muhimmanci a dukkanin bangarori a nahiyar Afirka.

Alh. Hamza Ibrahim Tsiga ya rike mukamai da dama na diflomasiyya a ofisoshin jakadacin Najeriya a kasashen duniya daban-daban, wanda kuma irin masaniya da kuma gogewa da yake da su a wannan bangaren, ya yi imanin cewa da yardar Allah zai samu nasara wajen gudanar da ayyukansa na bunkasa alaka da hulda a dukkanin bangarori na ci gaba tsakanin Najeriya da kuma kasar Iran, ta yadda kasashen biyu za su ci moriyar juna.

 

 

Tags