Iran Ta Yi Tir Da Hare-hare kan Masallatai A Afganistan
(last modified Sat, 21 Oct 2017 06:19:41 GMT )
Oct 21, 2017 06:19 UTC
  • Iran Ta Yi Tir Da Hare-hare kan Masallatai A Afganistan

Gwamnatin Jamhuriya Musulinci ta Iran ta yi tur da allawadai da jerin hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan masallatai a biranen Kabul da Ghor na kasar Afganistan.

Da yake bayyana takaicin kasarsa kan lamarin kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Bahram Qassemi, ya ce gwamnatin Tehran na jajanta wa al'ummar kasar ta Afganistan da isar da ta'aziyyarta ga iyalan wandanda lamarin ya yi ajalinsu.

Haka kuma Iran ta ce za ta ci gaba da taimaka wa gwamnatin ta Afganistan na ganin bayan ta'addanci.

Akalla mutum 60 ne suka rasa rayukansu a jerin hare-haren da aka kai kan masallatan biyu na kasar Afghanistan, kamar yadda jami'an kasar suka bayyana.

Harin mafi muni shi ne wanda ya yi ajalin kusan mutum 40 ciki har da mata da kananan yara a masalacin 'yan shia'a na kabul, sai kuma na gundumar Ghor inda mutane 20 suka yi shahada.