Sheikh Siddiqi: Makiya Sun Kirkiro Daesh (ISIS) Ne Don Kare H.K.Isra'ila
(last modified Fri, 15 Dec 2017 15:39:54 GMT )
Dec 15, 2017 15:39 UTC
  • Sheikh Siddiqi: Makiya Sun Kirkiro Daesh (ISIS) Ne Don Kare H.K.Isra'ila

Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar birnin Tehran, Hujjatul Islam wal Muslimin Kazim Siddiqi ya bayyana cewar makiya sun kirkiro kungiyar Da'esh (ISIS) ne da nufin tabbatar da tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila, to sai dai sun gagara cimma wannan bakar aniya ta su.

Hujjatul Islam wal Muslimin Kazim Siddiqi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a birnin Tehran a yau inda ya ce makiya al'ummar musulmi sun kirkiro kungiyar ta'addancin nan ta Daesh ne da nufin haifar da fitina a tsakanin musulmi don haramtacciyar kasar Isra'ila ta samu zaman cikin aminci da kwanciyar hankali, to sai dai sun gagara cimma wannan bakar aniyar  ta su, sannan kuma ta hakan Iran ta kara samun irin tasiri da fadi a ji da take da shi a yankin Gabas ta tsakiya.

Yayin da ya koma kan Palastinu da kuma birnin Qudus kuma, Na'aibin limanin Juma'ar ya bayyana cewar lamarin Palastinu shi ne babban kuma mafi muhimmancin lamurran duniyar musulmi, yana mai yin Allah wadai ga matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sanar da birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Sheikh Siddiqi ya kara da cewa babbar manufar makiya na haifar da rikici a duniyar musulmi ita ce shagaltar da musulmin da kansu don su manta da lamarin Palastinu wanda ya ce musulmi ba za su taba mancewa da wannan lamarin ba.