Iran / Rasha : Al'ummar Siriya Ne SuKe Da Hakkin Zabar Makomarsu
Shuwagabannin kasashen Iran da Rasha sun jaddada cewa al'umma kasar Siriya ne suke da hakkin zabar makomarsu
A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Rasha, shugaban kasar Iran Hassan Ruhani, ya bayyana cewa, Tehran na adawa da kasancewar duk wasu dakarun kasashen waje a kasar Siriya, ba tare da amincewar gwamnati da al'ummar kasar Siriya ba.
Dakta Ruhani ya kara da cewa rikicin dake faruwa a arewacin Siriya ba abu ne da zai gyara kowa ba, muna fatan duk kasashe zasu mutunta 'yanci da kuma hurumin kasar ta Siriya.
A daya bangare kuma shugaba Ruhani, ya yi maraba da taron tattaunawa na shuwagabannin kasashen Iran, Rasha, Da Iran a cikin tsarin hadin gwiwa don samar da zaman lafiya da yaki da ta'addanci a yankin.
A nasa bangare kuwa shugaba Vladimir Putin, ya ce kasarsa a shirye take domin karfafa alakarta da Iran a dukkan bangarori.