Jakadan MDD A Burundi Ya Nuna Damuwarsa kan Rikicin Kasar
(last modified Tue, 27 Feb 2018 08:09:06 GMT )
Feb 27, 2018 08:09 UTC
  • Jakadan MDD A Burundi Ya Nuna Damuwarsa kan Rikicin Kasar

Jakadan majalisar dinkin duniya na musamman a kasar Burundi Michel Kafando ya nuna damuwarsa yadda rikicin kasar Burunci yaki ci yaki cinyewa.

Majiyar muryar jamhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Michel Kafando yana fadawa komitin tsaro na Majalisar dinkin duniya a jita litinin kan cewa shiga tsakani da majalisar take yi babu son kai ko nuna bambanci a cikin bangarorin yan saiyasa da suke rikici da juna.

Kafando ya yi kira ga kungiyar tarayyar Afrika Au ta cika alkawalin da ta dauka na shiga tsakani don warware rikicin kasar ta Burundi kamar yadda tayi alkawari. 

Tun shekara ta 2015 ne rikicin siyasa ya barke tsakanin shugaban kasa mai ci Pierre Nkurunziza da jam'iyyun adawar kasar bayan da ya nace kan cewa sai ya tsaya takarar shugaban kasa karo na ukku wanda kundin tsarin mulkin kasar ta amince masa ba.