Kasar Zimbabwe Ta Jaddada Bukatar Bunkasa Alakarta Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
(last modified Thu, 05 Apr 2018 19:11:57 GMT )
Apr 05, 2018 19:11 UTC
  • Kasar Zimbabwe Ta Jaddada Bukatar Bunkasa Alakarta Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

Mataimakin shugaban kasar Zimbabwe ya bukaci bunkasa alaka a bangarori da dama da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A ganawar da ta gudana a birnin Harare fadar mulkin kasar Zimababwe tsakanin mataimakin shugaban kasar Zimbabwe na farko Constantino Chiwenga da jakadan kasar Iran Ahmad Irfaniyon a yau Alhamis: Jami'an biyu sun tattauna batun kyakkyawar alakar da ta hada kasashensu a tsawon tarihi musamman a lokacin gwagwarmayar neman yancin kan kasar Zimbabwe daga turawan mulkin mallaka tare da jaddada bukatar bunkasa alaka a tsakanin kasashensu a bangarori da dama.

Constantino Chiwenga ya bayyana cewa akwai fage masu yawa da kasashen Iran da Zimbabwe zasu gudanar da taimakekkeniya a tsakaninsu musamman a harkar kasuwanci.

A nashi bangaren jakadan kasar Iran a Zimbabwe Ahmad Irfaniyon ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka samu canji gwamnatin a Zimbabwe ba tare da zubar da jini ba tare da jaddada aniyar Iran na ganin ta bunkasa alaka da dukkanin kasashen nahiyar Afrika musamman Zimbabwe.

A ranar 24 ga watan Nuwamban shekara ta 2017 da ta gabata ce matsin lamba ya tilastawa Robert Mugabe dan shekaru 94 a duniya yin murabus daga kan karagar shugabancin Zimbabwe, inda tsohon mataimakinsa Emmerson Mnangagwa ya maye gurbinsa.