Rasha: Wajibi Ne A Kare Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
(last modified Mon, 07 May 2018 18:57:32 GMT )
May 07, 2018 18:57 UTC
  • Rasha: Wajibi Ne A Kare Yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergey Ryabkov ne ya bayyana haka a yau litinin sannan ya kara da cewa; Rasha tana son ganin dukkanin bangarorin yarjejeniyar sun ci gaba da aiki da ita

Ryabkov ya yi ishara da yadda kasashen Amurka da Faransa suke sukar yarjejeniyar sannan ya ce; Wannan irin halayya za ta raunana yarjejeniyar wacce duniya ta amince da ita.

Kasashen da suke bangarorin yarjejeniyar da su ka kunshi Rasha, Tarayyar turai, Sin, suna jaddada wajabcin ci gaba da aiki da ita.

Amurka ta bakin shugabanta Donald Trump ne ke shirin yi wa yarjejeniyar kafar angulu. Tuni dai jamhuriyar musulunci ta Iran ta sanar da cewa za ta mai da martani akan matakin na Amurka.