IRGC: Ranar Kudus Ranar Hadin Kan Musulmi Da Goyon Bayan Palastinu Ce
(last modified Thu, 07 Jun 2018 11:15:29 GMT )
Jun 07, 2018 11:15 UTC
  • IRGC: Ranar Kudus Ranar Hadin Kan Musulmi Da Goyon Bayan Palastinu Ce

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran (IRGC) sun bayyana Ranar Kudus ta duniya a matsayin ranar hadin kan al'ummar musulmi da kuma nuna goyon bayan ga al'ummar Palastinu da ake zalunta.

Dakarun kare juyin juya halin Musuluncin sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar a yau din nan Alhamis don girmama ranar Kudus ta duniya da za a gudanar a gobe Juma'a inda suka bayyana cewar: Sakamakon bayyanar da Ranar Kudus ta duniya da marigayi Imam Khumaini (r.a) shekaru 39 da suka gabata a halin yanzu batun Palastinu da maganar 'yanto Kudus ya zamanto wani lamari na kasa da kasa.

Dakarun kare juyin, cikin sanarwar ta su sun kara da cewa: Ranar Kudus ta duniya a bangare guda wata ranar ce ta hadin kan al'ummar musulmi da kuma nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu, a bangare guda kuma haramtacciyar kasar Isra'ila da masu goya mata baya a kullum sai kara rauni suke yi.

A gobe Juma'a ne ake sa ran za a gudanar da bukukuwan Ranar Kudus ta duniya don amsa kiran marigayi Imam Khumaini wanda ya sanya ranar juma'ar karshe ta watan Ramalana a matsayin Ranar Kudus ta duniya don nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu.