Iran : Rohani Ya Taya Erdogan Murnar Lashe Zabe
Shugaba Hassan Rohani na Jamhuriya Musulinci ta Iran, ya taya, Recep Tayyip Erdoğan, murna kan sake zabensa a wani wa'adin mulki kasar Turkiyya.
A wani sako da fadar shugaban kasar Iran ta fitar, Shugaba Rohani, ya yi fatan karfafa kyakyawar dangantaka ta amintaka tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Rohani ya kuma yi fatan fadada dangantaka ta tsakanin hukumomin kasashen biyu, kan batutuwan da suka shafi ci gaban yankin da kuma kasa da kasa domin shawo kan matsalolin da ake fama dasu, da bunkasa zaman lafiya da kawo kwanciyar hankali don samun makoma mai kyau a yankin.
Dakta Rohani ya kuma yi wa twakwaransa fatan alkhairi da kuma samar da ci gaba ga dukkan al'ummar Turkawa.
Recep Tayyip Erdoğan, ya dai lashe zaben shugabancin kasar ta Turkiyya da aka kada kuri'arsa a ranar Lahadi data gabata da kusan kashi 53% na yawan kuri'und a aka kada a cewar kamfanin dilancin labaren kasar « Anadolu».