Shugaba Rouhani Ya Aike Da Sako Zuwa Takwaransa Na Tunusiya.
(last modified Thu, 05 Jul 2018 06:41:54 GMT )
Jul 05, 2018 06:41 UTC
  • Shugaba Rouhani Ya Aike Da Sako Zuwa Takwaransa Na Tunusiya.

A yayin ganawarsa da Shugaban kasar Tunusiya Al-Baji Qa'ed al-Sabsi, mataimakin Ministan harakokin wajen Iran kan harakokin siyasa ya meka maka sakon Shugaba Hasan Rouhani

Hasan Jabiri Ansari mataimakin ministan harakokin wajen Iran a harakokin siyasa dake a matsayin manzon musaman na shugaban kasar Iran zuwa kasar Tunusiya, ya gana da Shugaban kasar Al-Baji Qa'ed al-Sabsi a jiya Laraba, inda ya meka sakon shugaba Rouhani.

Shidai wannan sako bayyani ne na karshe halin da ake ciki a game da yarjejjeniyar nukiliyar Iran na zaman lafiya da kasashen Turai bayan ficewar kasar Amurka daga cikinta, 

Bayan gabatar da wannan sako mataimakin ministan harakokin wajen Iran ya bayyana kokarin da kasar Iran ke yi na magance matsalolin yankin gabas ta tsakiya cikin ruwan sanhi, da kuma kudurin kasar na bunkasa alakar siyasa, al'adu da tattalin arziki da kasar ta Tunusiya.

A nasa bangare, Shugaban kasar Tunusiya Al-Baji Qa'ed al-Sabsi ya bayyana godiyarsa ga Shugaban kasar Iran, sannan ya yi ishara da girman tahiri na al'adun kasar Iran, da kuma 'yan siyasar kasarsa a game da harakokin da suka shafi yankin gabas ta tsakiya harda ma kasa da kasa, sannan ya bayyana fatansa na ganin kasashen biyu sun amfana da alakar dake tsakaninsu.