Zarif: Manyan Kasashe Sun Jaddada Wajabcin Yin Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliyan Iran
(last modified Fri, 06 Jul 2018 17:31:33 GMT )
Jul 06, 2018 17:31 UTC
  • Zarif: Manyan Kasashe Sun Jaddada Wajabcin Yin Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliyan Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa; dukkanin bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya, sun jaddada wajabcin ci gaba da yin aiki da ita kamar yadda aka rattaba hannu a kanta.

Zarif ya bayyana hakan ne da yammacin yau, bayan kammala zaman taro da ministocin harkokin wajen kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya suka gudanar yau a birnin Vienna na kasar Austria.

Zarif ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a kare wanann yarjejeniyar da kuma yin aiki da dukkanin abubuwan da ta kunsa bayan ficewar Amurka daga cikinta.

Dukkanin ministocin harkokin waje na kasashen Iran, Faransa, Birtaniya, Jamus gami da Rasha da kuma China da kungiyar tarayyar turai sun samu halartar zaman na yau Juma'a.