Fadada Ayyukan Kiwon Lafiya Tsakanin Iran Da Senegal
Jakadan Iran a birnin Dakar na kasar Senegal ya bayyana cewa, kasashen biyu suna aiki wajen kara bunkasa ayyukan hadin gwiwa a bangaren kiwon lafiya da kuma magunguna.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya habarta cewa, jakadan Iran a kasar Senegal Ainullah Qashqawi, tare da ministan kiwon lafiya na Senegal Abdoulaye Diouf Sarr, sun jaddada cewa kasashen biyu za su ci gaba da aiki tare wajen fadada ayyuka na kiwon lafiya da kuma samar da magunguna.
Jakadan na Iran a Senegal ya ce; bisa la'akari da gagarumin ci gaban da kasar Iran ta samu a bangaren kera na'urori na ayyuka a bangaren kiwon lafiya, ba za ta yi kasa a gwiwa wajen taimaka ma kasar Senegal a wannan fage ba, domin kara bunkasa ayyukan kiwon lafiya da kuma asibitocin kasar ta Senegal.
Haka nan kuma jakadan Iran ya ce a bangaren magunguna da Iran take samarwa, Senegal za ta kasance daya daga cikin kasashen da za su rika amfana da yarjejeniyar shigar da magunguna a kasar daga Iran, kamar yadda Iran kuma take da niyyar kafa kamfanonin yin magunguna a kasar Senegal nan ba da jimawa ba.