Zarif: Amurka Ta Zama Saniyar Ware Bayan Ficewa Daga Yarjejeniyar Nukiliya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad zarif ya bayyana cewa, Amurka ta mayar da kanta saniyar ware, tun bayan da ta fice daga yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya.
A lokacin da yake zantawa da tashar talabijin din kasar Iran, Zarif ya bayyana cewa, ko shakka babu matakin da Amurka ta dauka na ficewa daga yarjejeniyar nukiliya kan shirin Iran da duniya wadda dukkanin kasashen duniya suka amince da ita, hakan babban kure ne na siyasa Amurka ta tafka.
Zarif ya ce a halin yanzu Amurka ce kawai ta zama saniyar ware a kan wannan batu, domin dukkanin bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar suna nan suna mutunta ta da kuma yin aiki da ita.
An dai rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya a cikin shekara ta 2015, amma a cikin wannan shekara shugaban Amurka Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar, domin yin amfani da hakan wajen ci gaba da matsa lamba kan Iran.