Shugaban Rasha Ya Iso Birnin Tehran
Shugaban kasar Rasha Viladimin Putin ya iso birnin tehran domin halartar taro kan birnin Idlib na kasar Siriya
A marecen wannan juma'a ce shugabannin kasashen Iran da Rasha da kuma Turkiyya za fara gudanar da taro a birnin Tehran domin fayyace makomar lardin Idlib, wanda shi ne tungar karshe da ta rage a hannun ‘yanta'addar kasar Syria.
Wani jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Iran Sadiq Husain Jabiri Ansari ya ce; Tuni an kammala tsara bayanin bayan taron na bangarori uku a Tehran
Jabir Ansari ya kuma ce; Yankin Idlib ne kadai wurin da ya rage a kasar Syria da yake a karkashin 'yan ta'adda.
Har ila yau, jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce dukkanin kasashen uku da suke taro a Tehran suna fuskatar takunkumi daga kasar Amurka.
Kwararru daga kasashen uku sun yi zama na musamman anan Tehran inda su ka fitar da bayanin da zai zama na bayan taron shugabannin kasashen.