Tehran: An Kammala Zaman Taron Shugabannin Kasashen Rasha, Turkiya Da Iran
(last modified Fri, 07 Sep 2018 18:07:43 GMT )
Sep 07, 2018 18:07 UTC
  • Tehran: An Kammala Zaman Taron Shugabannin Kasashen Rasha, Turkiya Da Iran

An kammala zaman taron shugabannin kasashen Rasha, Iran da kuma Turkiya, wanda aka gudanar yau Juma'a a birnin Tehran na kasar Iran a kan batun rikcin kasar Syria, da kuma ci gaba da nemo hanyoyin warware rikicin.

Dukaknin shugabannin kasashen Uku, wato Hassan Rauhaini na Iran da kuma Vladimir Putin na Rasha gami da Rajab Tayyib Erdogan na Turkiya, sun fitar da bayanin bayan taron nasu wanda ya kunshi bangarori 12, da ke tabbatar da wajabcin kasancewar Syria dunkulalliyar kasa guda.

Hakan nan kuma bayanin bayan taron ya jaddada wajabcin ci gaba da yaki da 'yan ta'adda musamman kungiyoyin daesh da Nusra Front.

Dangane da batun Idlib kuwa, taron ya mayar da hankali ne kan yadda za a kammala tsarkake yankin ba tare da hakan ya cutar da fararen hula da 'yan ta'adda suke garkuwa da su a cikin yankin ba.

Haka nan kuma bayanin ya kirayi majalisar dinkin duniya da ta taka muhimmiyar rawa wajen taimaka ma 'yan gudun hijira da 'yan ta'adda suka kore su daga yankunansu  cikin  kasar ta Syria, wadanda suka tsere zuwa kasashe makwabta, tare da taimaka musu wajen dawowarsu kasarsu.