Sep 22, 2018 16:47 UTC
  • Iran : Jagora Ya bukaci A Binciko Wadanda Suka Shirya Harin Ahwaz

Bayan harin ta'addancin da aka kai a garin Ahwaz yau Asabar, Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan shahidan da lamarin ya rusa dasu.

Jagoran ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ofishinsa ya fitar a yau, yana mai cewa 'yan ta'adda marasa imani da tausayi dake samun taimakon makiya, sun bude wa wadanda basu ji basu gani ba da suka hada da mata da yara wuta, a don haka wannan yauni ne da rataya a wuyan ma'aikatar leken asirin kasar data yi aikinta cikin tsanaki ta tantance ta kuma binciko suwa keda hannu a wannan harin domin gurfanar dasu gaban kotu.

Ya kara da cewa a cikin bakaken zukatansu, basa iya jurewa ganin karfin da Iran take da shi a cikin faretin sojojinta.

Ya ce wannan harin allawadai da aka kai, manunuya ce ta furucin da wasu kasashen yankin bisa goyan Amurka ke yi, na ganin sun haifar da fitina da tashin hankali a wannan kasa, a don haka kasar Iran a koda yaushe zata ci gaba da dakile duk wani makircinsu.

Wadannan a cewar Jagoran su ne makaryata da kulun suke ikirarin kare hakkin bil adama.

Tags