Rasha:Ci Gaba Da Kare Yarjejeniyar Nukiliya Yana Da Matukar Muhimmanci
(last modified Wed, 26 Sep 2018 19:09:05 GMT )
Sep 26, 2018 19:09 UTC
  • Rasha:Ci Gaba Da Kare Yarjejeniyar Nukiliya Yana Da Matukar Muhimmanci

Babban jami'i mai kula hana yaduwar makaman Nukiliya a duniya a ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha, Vladimir Yermakov ya ce kasashen da suke ci gaba da riko da yarjejeniyar suna ba ta matukar muhimmanci

 Vladimir Yermakov ya kara da cewa: Amurka tana nuna damuwa akan masaniyar da Iran take da ita dangane da fasahar makamashin Nukiliya, alhali kwararru sun tabbatar da cewa shirin na Iran ba shi da wata fuska ta soja.

Jami'in na kasar Rasha ya kara da cewa; Kwararru na hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa sun tabbatar da fuskar zaman lafiya da sulhu na shirin makamashin Nukiliyar Iran, wanda a bisa haka ne aka yi yarjejeniyar Nukiliya.

 Vladimir Yermakov ya kuma ce; Babu wata kasa a duniya wacce ake sanya idanu akan shirinta na Nukiliya na zaman lafiya kamar Iran, kuma har yanzu ba a sami wata matsala ba.

Kasashen Faransa da Rasha da Sin da Jamus da tarayyar turai sun jaddada muhimmancin ci gaba da aiki da yarjejeniyar Nukiliyar ta Iran.