Iran Ta Hallaka 'Yan Ta'adda 40
Babban Kwamandan tsaron saman kasar Iran ya sanar da cewa harin makami mai Linzami na baya-bayan da kasar ta kai kan 'yan ta'adda a gabashin Furat na kasar Siriya ya hallaka 'yan ta'adda akalla 40.
Brigadier Janar Amir Ali Haji Zaadeh babban kwamandan Dakarun sama na kare juyin juya halin Musulinci na Jamhuriya Musulinci ta Iran (IRGC) ya nuna hotunan yadda makamai masu Linzami suka samu wuraren 'yan ta'addar a Bukmal dake gabashin Furat na kasar Siriya, inda ya ce dukkanin makamai da suka halba sun samu wuraren da suka yi nufi, kuma labarai sun tabbatar musu da cewa akalla 'yan ta'adda 40 suka hallaka ciki kuwa har da wasu kwamondojinsu.
Brigadier Janar Haji Zaadeh ya ce duk da cewa akwai sansanin Sojojin Amurka a kusa da idan suka kai harin, amma babu wani makami da ya sauka kan sansanin sojojin Amurkan, wanda kuma hakan ke nuna karfi da kwarewa na dakarun kare juyin juya halin Musulinci na Jamhuriya Musulinci ta Iran.
Har ila yau Brigadier Janar Haji Zaadeh ya ce wannan shi ne karon farko da dakarun kare juyin juya halin musulinci ta Iran suka yi amfani da jirgi maras matuki wajen kai hari, baya ga makamai masu linzamin.
A jijjifin safiyar Litinin din da ta gabata ce dakarun tsaron sararin samaniya kasar Iran suka kai hari jirgin yaki maras matuki da makamai masu Linzami samfarin "Zulfikar da "Kiyam" inda suka bi ta sararin samaniyar Iraki, kafin su aukawa babban sansanin 'yan ta'addan a yankin Deir ez-Zor na kasar Iraki.
Wannan harti dai na a matsayin fara maida martani na harin ta'addancin da aka kai na ranar 22 ga watan Satumba a yayin wani faretin soji a garin Ahwaz dake yankin Khouzistan na kudancin kasar ta Iran, da ya yi sanadiyar shahadar mutane akalla 25 tare da raunana wasu da dama na daban.