Bahram Qassemi:Zaben Afganistan Ya Nuna Gagarimin Sauyi A Bangaren Tsaro
Kakakin ma'aikatar harakokin wajen Iran ya taya al'ummar kasar Afganistan murnar zaben 'yan majalisa a kasar, sannan ya ce wannan babban sauyi ne aka samu a bangaren tsaro da kuma ci gaban kasar.
A jiya Laraba kakakin ma'aikatar harakokin wajen Iran ya taya gwamnati da al'umma kasar Afganistan murna na zaben 'yan Majalisar dokoki da kuma bayyana fatansa na samun gagarumin sauyi na makomar kasar musaman ma wajen magance matsaloli da kuma tabbatar da tsaro da sulhu gami da bunkasar kasar a yayin fara aiki da sabuwar majalisar.
Duk da irin barazar tsaro da kasar ke fama da shi, a ranaikun 20 da 21 na wannan wata na Oktoba da muke ciki , al'ummar kasar Afganistan suka gudanar da zaben 'yan majalisa a jahohi 32 na kasar.
Abdul-Badi'i Sayad, shugaban kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar Afganistan ya ce a ranar 6 ga watn Nuwamba ne za a fara firar da sakamkon zaben na ficin gadi, sannan a ranar 20 ga watan Dicemba za a bayar da sakamakon karshe.