Yerjejeniyar Nukliyar Kasar Iran Ta Maida Amurka Saniyar Ware A Duniya.
(last modified Mon, 28 Jan 2019 11:58:38 GMT )
Jan 28, 2019 11:58 UTC
  • Yerjejeniyar Nukliyar Kasar Iran Ta Maida Amurka Saniyar Ware A Duniya.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa ficewar Amurka daga yerjejeniyar Nukliyar Iran ta shekara ta 2015 ya maida Amurka saniyar ware a duniya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kalato Muhammad Jawad Zarif yana fadar haka a yau Litinin ya kuma kara da cewa bayan ficewar Amurka daga yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran a cikin watan Mayun shekarar da ta gabata, Amurka ta yi kokarin hada kai da kasashen duniya su yiwa Iran taron dangi amma ta kasa yin hakan. Wannan ya maida ita saniyar Ware a duniya. 

Minisyan ya kara da cewa ficewar Amurka daga wasu yerjeniyoyin kasa da kasa wadanda suka hada da na Paris kan dumamayar yanayi, da budaddiyar kasuwannin duniya da sauransu duk sun bayyana cewa Amurka bata mutunta dokokin kasa da kasa wadanda suke tabbatar da zaman lafiya a duniya.

A bangaren kudu kuma ministan ya nuna damuwarsa da yadda gwamnatin hadaddiyar daular Larabawa wato Emmerate take cutar da masu canjin kudade Iraniya wa a kasar duk da cewa kasar tana da dangantaka mai kyau da kasar Iran. Zarif ya ce gwamnatin kasar Iran zata dauki matakan da suka dace don kare mutanen kasarsa.