Jarogora Ya Isar Ta Sakon Ta'aziyarsa Ga Iyalan Shahidan Sistan Baluchestan
Jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyeed Aliyul Khaminae, ya gabatar da ta'aziyarsan ga iyalan shahidan dakarun kare juyin juya halin musulunci a kasar wadanda suka yi shahada a lardin sisatan Buluscistan a jiya da dare.
Shafin yanar gizo na ofishin jagoran ya bayyana a yau Alhamis kan cewa jagoran ya isar da ta'aziyarsa ga iyalan shahidan da kuma dakarun juyin juya hali kan wannan rashin, har'ila yau da tayasu murnan shahadan da wadannan matasa muninai suka samu sanadiyar kissansu da makiya suka yi.
A dayan bangaren kuma jagoran ya bayyana cewa babu shakka akwai hannun makiya a cikin gida wadanda suka samun tallafin kasashe makonta da ma na nesa a harin na jiya da dare.
A jiya Laraba da dare ne wata motar Bus dauke da dakarun kare juyin juya halin musulunci tsakanin garin Zahidan da kuma Khosh na lardin Sistan Bulusistan suka yi karo da wata motan yan konan bakin wake wanda ya tarwatsa motar, ya kai kuma ga shahadar sojoji na dakarun kare juyin juya halin musulunci 27 ya kuma raunata wasu 13.
Jagoran ya bukaci jami'an gwamnatin da abin ya shafa su bi kadin wannan lamarin har sai sun gani wadanda suke da hannu cikinsa .
Sai dai wata kungiya wacce ake kira "Sojojin Zalunci" wacce kuma take samun goyon bayan kasar Saudia ta dauki alhakin kai harin na jiya.