Afrika Ta Kudu Za Ta Kara Fadada Harkokin Kasuwanci Tare Da Iran
(last modified Sat, 23 Feb 2019 06:59:53 GMT )
Feb 23, 2019 06:59 UTC
  • Afrika Ta Kudu Za Ta Kara Fadada Harkokin Kasuwanci Tare Da Iran

Gwamnatin kasar Afrika ta kudu na shirin kara fadada harkokin kasuwancinta tare da kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, jakadan kasar Afrika ta kudu a kasar Iran Wika Mazuri Kumalo ya bayyana cewa, kasarsa na shairin kara fadada harkokin kasuwanci tare da kasar Iran.

Kumalo ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da ya kai ziyara a birnin Yazd na kasar Iran, inda ya bayyana cewa akwai kyakyawar dangantaka ta kasuwanci da sauran harkokin tattalin arziki tsakanin Iran da kuma Afrika ta kudu.

Ya ce duk da takunumin da Amurka ta kakaba wa kasar ta Iran, kasarsa na shirin ganin ta kara karfafa wannan hulda da sauran batutuwa da suka danganci yawon bude ido, da kuma musayar ilimin kimiyya da fasaha a tsakanin kasashen biyu, kamar yadda za su kara karfafa ayyukan hakar ma'adanai.

Kasar Afrika ta kudu dai na daga cikin kasashen nahiyar Afrika da suke da kyakkywar alaka ta kasuwanci da harkoki na tattalin arziki tare da kasar Iran.