Shugaba Ruhani: Akwai Bukatar Aiki Tare Wajen Fada Da Ta'addanci
(last modified Tue, 12 Apr 2016 17:23:27 GMT )
Apr 12, 2016 17:23 UTC
  • Shugaba Ruhani: Akwai Bukatar Aiki Tare Wajen Fada Da Ta'addanci

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar ayyukan ta'addanci suna ci gaba da zama babbar barazana ga zaman lafiyar dukkanin kasashen duniya, don haka akwai bukatar aiki tare tsakanin kasashen duniya wajen fada da wannan annobar.

Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da firayi ministan kasar Italiya Matteo Renzi wanda yake ci gaba da ziyarar aiki a kasar Iran inda ya ce: Ya kamata masu goyon bayan kungiyoyin ta'addanci su san cewa wadannan kungiyoyi ne dai barazana da kuma cutarwa ne ga dukkanin bil'adama, yana mai cewa kashe duk wani mutum a ko ina yake kuwa babban bala'i ne.

Shugaban na Iran ya kara da cewa a halin yanzu dai akwai bukatar hadin kai tsakanin dukkanin al'ummomi wajen fada da ta'addanci da tsaurin ra'ayi na addini a duk fadin duniya, yana mai sake jaddada kudurin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na hada kai da dukkanin kasashen duniya wajen cimma kudurin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi na kawo karshen amfani da karfi da tsaurin ra'ayi a duniya a 2013.

Shi dai wannan kudurin, shugaba Ruhanin ne ya gabatar da shi a taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 2013 inda kuma aka amince da shi.

A yau Talata ce firayi ministan kasar Italiyan Matteo Renzi ya kawo ziyarar aiki nan Iran don karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma bin sahun yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma a kwanakin baya a lokacin da shugaba Ruhani ya kai ziyara kasar Italiya