Shugaba Jacob Zuma Ya Ziyarci Ayatollah Khamenei A Tehran
Apr 24, 2016 19:21 UTC
Shugaba Jacob Zuma ya ziyarci jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei a gidansa da ke Tehran.
A yammacin yau Lahadi shugaba Jacob Zuma na kasar Afirka ta kudu tare da rakiyar shugaba Rauhani, ya ziyarci jagoran juyin Islama na kasar Iran Ayatollah Khamenei a gidansa da ke Tehran, inda jagoran ya sheda masa cewa, ya zama wajibi kan kasashe masu 'yancin siyasa, su hada karfi da karfe domin taka birki ga masu girman kai da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya.
yayin da shugaba Zuma ya nuna gamsuwarsa tare da jinjinawa kasar ta Iran, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da yin aiki kafada da kafada tare da Iran domin ci gaban al'ummominsu.
Tags