Adadin mutanan da suka rasu ya karu a kudancin Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10321-adadin_mutanan_da_suka_rasu_ya_karu_a_kudancin_yemen
Adadin Mutanan da suka rasu sandiyar harin kunar bakin wake a kudancin Yemen ya karu
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Aug 29, 2016 12:23 UTC
  • Adadin mutanan da suka rasu ya karu a kudancin Yemen

Adadin Mutanan da suka rasu sandiyar harin kunar bakin wake a kudancin Yemen ya karu

A wani sabon rahoton da tashar telbijin din Arabie News ta fitar ta ce adadin mutanan da suka rasa rayukansu sandiyar harin kunar bakin waken da aka a wurin koyon aikin soja na birnin Adan ya haura zuwa 71 yayin da adadin wadanda suka jikkatan ya haura zuwa 98.

Majiyar  tsaron kasar ta Yemen ta bayyana cewa an kai harin ne da wata mota  shake  da bama bamai a wata cibiyar sojoji sabbin dauka da ke a bakin garin birnin Aden.

Kudancin yankin Adan na kalkashin ikon Dakarun dake goyawa koraren shugaban Kasar ta Yemen Abdu Rabbahu Hadi Mansuri. Harin wuce gona da iri da kawancen kasashen Larabawa bisa Jagorancin Masarautar Ali sa'oud shi ne ya janyo kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Alqa'ida da kuma IS suka samu gindin zama a wasu yankuna na kasar ta Yemen.

A bangare guda Jiragen yakin Kawancen Saudiya sun yi ruwan bama-bamai a wasu yankuna na Jihar Sa'ada dake kalkashin ikon Mayakan Alhutsi, a matsayin mayar da martani Dakarun kasar ta Yemen tare da na sa kai sun halba makamai masu lizzami a wuraren taruwar Sojojin Saudiya dake barikin Soja na Abu Hamdan na jihar Najran dake kudancin Saudiyar.