Ansarullah Sun Nuna mamakinsu Akan Shirun Kungiyoyin Kasa Da Kasa
Feb 20, 2016 09:47 UTC
Wani jami'i a kungiyar Ansarulla ta kasar Yemen ya bayyana mamakinsa akan sirun da duniya ta yi dangane da killace kasar ta Yemen.
Aliyul al-Bakhty wanda mamba ce a kwamitn shawar na kungiyar ta Ansarullah ya ce; Idan har aka ci gaba da yin shiru akan kilace kasar ta Yemen daa aka yi, to hakan zai tabbatar da mummunar rawar da Majalsiar dinkin duniyar ta taka.
Jami'in na kungiyar Ansarullah ya kuma yi ishara da cewa; Da dama daga cikin jiragen ruwa masu dauke da kayan agaji zuwa kasar, sun kasa isa saboda killacewar da Saudiyya ta yi Yemen.
Watanni kusan 11 kenan da Saudiyya ta shelanta yaki akan Kasar Yemen, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka da kuma jikkata wasu.
Tags