Tsagaita wuta na sa'o'i 72 A kasar Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10723-tsagaita_wuta_na_sa'o'i_72_a_kasar_yemen
Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da cewa Saudiya ta amince da yarjejjeniyar tsagaita wuta na tsahon sa'o'i 72 a kasar Yemen
(last modified 2018-08-22T06:58:53+00:00 )
Sep 07, 2016 06:20 UTC
  • Tsagaita wuta na sa'o'i 72 A kasar Yemen

Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da cewa Saudiya ta amince da yarjejjeniyar tsagaita wuta na tsahon sa'o'i 72 a kasar Yemen

A yayin ganarwarsa da Ministan harakokin saudiya Adil Jubair da kuma mataimakin mai jiran gado na masarautar Saudiya Muhamad bn Salman, Saktaren harakokin wajen Amurka Jean Kery ya bayyana cewa sun cimma matsaya na tsagaita wuta sa'o'i 72 a kasar Yemen.

Mai magana da yawun Ma'aikatar harakokin wajen Amurka Jonh Kerby ya ce tattaunawar an gudanar da ita a gefen taron kasashe masu karfin arzikin tattalin arziki na Duniya da ake kira da G20 dake gudana a kasar China.

An cimma wannan yarjejjeniya ne domin bayar da dama ga masu kai Agaji na Majalisar Dinkin Duniya su gudanar da aiyukan su a cikin kasar.