Sojojin Saudiyya Sun Kashe Fararen hula 17 A Kasar Yamen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i11125-sojojin_saudiyya_sun_kashe_fararen_hula_17_a_kasar_yamen
Jiragen yakin Saudiyya Sun kashe Fararen hular Yamen 17 a yau juma'a.
(last modified 2018-08-22T06:58:56+00:00 )
Sep 16, 2016 14:26 UTC
  • Sojojin Saudiyya Sun Kashe Fararen hula 17 A Kasar Yamen

Jiragen yakin Saudiyya Sun kashe Fararen hular Yamen 17 a yau juma'a.

A yau juma'a jiragen yakin Saudiyya sun kai hari a yankunan San'a da Ma'arib  na kasar Yamen, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula 17.

Tashar telbijin din al-masirah ta kasar Yamen ya bada labarin cewa; Jirgin yakin Saudiyya ya kai hari akan wata motar matafiya a yankin alotdeh a garin Kholan da ke gundumar San'aan, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 10.

Jiragen yakin na Saudiyyar sun kuma kai wani harin a yankin Wadi al-Zagan da ke garin Sarwah a gundumar Ma'arib, da ya ci rayukan mutane 5.

A garin Gorgumar ma dai jiragen yakin na Saudiyya sun kai wasu hare-haren a yau juma'a.