Bukatar Majalsar 'yan siyasar Yemen ga Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Majalisar Koli na 'yan siyasar yemen ya bukaci a dauki matakin gaggauwa domin kawo karshen hare-haren wuce gona da iri da masarautar Ali sa'oud ke kaiwa kana kasar sa
Tashar telbijin din Almayadin ta kasar Labnon ta habarta cewa a jiya Alhkamis shugaban Majalisar koli ta 'yan siyasar kasar Yemen Salih Assamad ya aike da wasika zuwa babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon inda ya bukaci Majalisar da ta dauki matakan gaggauwa da zai tilastawa magabatan Saudiya su kawo karshen killacewa da yakin wuce gona da irin kan Al'ummar kasar yemen.
A cikin wasikar, Shugaban Majalisar ya ce daga cikin Al'ummar kasar a kwai wadanda suke cikin yanayi na rashin lafiya suna bukatar fita kasashen wajen domin neman magani, Daliban kasar dake kasashen wajen na son dawowa gida to amma ganin takunkumin da masarautar Ali sa'oud ta kakabawa filin sauka da tashi na kasar Marasa lafiya ba za iya fita neman magani ba, haka zalika daliban ba za su iya fita ko kuma dawowa cikin kasar ba.
Tun a watan Maris din shekarar 2015 ne magabatan Saudiyar tare da hadin gwiwar wasu kasashen larabawa da Amurka suka fara kai hare haren wuce gona da irin a kan Al'ummar kasar ta Yemen.