Jagoran Ayyukan Jin Kai Na MDD Na Ziyara A Yemen
-
Stephen O'Brien na ganawa da wasu 'yan Yemen
Jagoran ayyukan jin kai na MDD, Stephen O'Brien, ya soma wata ziyara aiki ta kwanaki uku a kasar Yemen.
A yayin ziyara tasa Mista O'Brien, zai gana da jami'an kasar ta Yemen dana kungiyoyin agaji domin tattauna halin da fararen hula ke ciki a wannan kasa.
Hakazakila Mista O'Brien zai isa a yankin Hobeida inda matsalar karamcin abunci tayi kamari sosai saboda yakin da aka shafe sama da watanni 19 anayi a kasar ta Yemen.
kimanin mutane milyan uku ne ke bukatar agajin gaggawa a kasar Yemen.
Wannan ziyara ta Mr O'Brien na zuwa ne a daidai lokacinda wakilkin musamen na MDD kan rikicin kasar ta Yemen Ismaïl Ould Cheikh Ahmed shi ma yake wata ziyara a kasar Saudiyya, inda ya gana da shugaban kasar ta Yemen din mai murabus, Abd Rabbo Mansour Hadi a wunkurin farfado da tattaunawar sulhun da aka dakatar a watan Agusta a Kowait tsakanin bangarorin dake rikici a kasar ta Yemen.
Alkaluma daga MDD sun nuna cewa sama da mutane 6,600 ne suka rasa rayukansu, kana wasu kusan milyan uku suka kauracewa muhallansu saboda yakin daya ki yaki cinyewa a kasar ta Yemen.