Sayyid Nasrallah: Gwagwarmaya Ta Hana Makiya Cimma Manufofinsu
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar kungiyoyin gwagwarmaya sun hana makiyan al'umma cimma manufofin da suke son cimmawa.
Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wajen taron daren farko na watan Muharram da kungiyar take gudanarwa inda ya ce: nasara ita ce samun damar hana makiyi cimma manufofinsa. Don haka a lokacin da kungiyar gwagwarmaya ta samu nasarar hana makiya cimma manufofinsu, to a hakikanin gaskiya ta yi nasara kenan.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da abin da ya faru a Karbala, shugaban kungiyar Hizbullah din ya ce: A Karbala dai sansanoni ne guda biyu, kowane guda daga cikinsu yana da manufar da yake son cimmawa. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa babbar manufar Imam Husain (a.s) a Karbalan ita ce kare addinin Musulunci daga gurbata sannan kuma ya cimma wannan manufa sakamakon tsayin daka.
A duk shekara kungiyar Hizbullah din ta kan gudanar da irin wadannan tarurruka don tunawa da abin da ya faru a Karbala din inda manyan jami'an kungiyar suke gabatar da jawabai da tabo bangarori daban-daban na lamarin Karbalan.