Sojojin Yamen Sun Kai Hare-Haren Daukan Fansa Kan Kasar Saudiyya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i11929-sojojin_yamen_sun_kai_hare_haren_daukan_fansa_kan_kasar_saudiyya
Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun kai hare-haren daukan fansa kan sansanonin sojin kasar Saudiyya da suke lardunan kudancin kasar ta Saudiyya.
(last modified 2018-08-22T06:59:01+00:00 )
Oct 03, 2016 14:24 UTC
  • Sojojin Yamen Sun Kai Hare-Haren Daukan Fansa Kan Kasar Saudiyya

Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun kai hare-haren daukan fansa kan sansanonin sojin kasar Saudiyya da suke lardunan kudancin kasar ta Saudiyya.

Tashar talabijin na Al-Masiriyya ta kasar Yamen ta watsa rahoton cewa: Sojojin Yamen da hadin gwiwar dakarun sa-kai na kasar sun kaddamar da hare-haren daukan fansa da makamai masu linzami kan muhimman wajaje a garuruwan Najran da Jizan da suke kudancin kasar Saudiyya, inda suka yi nasarar tarwatsa sansanonin soji hudu tare halaka sojojin Saudiyya masu yawa.

Har ila yau sojojin Yamen da dakarun sa-kan sun takawa sojojin Saudiyya da na kawayenta burki a kokarin da suke yi na kwace iko da garin Ma'arib a tsakiyar kasar ta Yamen, kuma a dauki ba dadin da aka yi a tsakanin bangarorin biyu sojojin na Yamen sun samu nasarar halaka sojojin hayar Saudiyya 21 tare da jikkata wasu 31 na daban.