An Kashe Sojojin Saudiyya Da Dama A Kasar Yamen
Jami'an Tsaron Yamen Sun Kashe Manyan Jami'an Saudiyya
Jami'an Tsaron Yamen Sun Kashe Manyan Jami'an Saudiyya a yankin Ma'arib.
Tashar Telbijin din al-masirha ta Yamen ta ambaci cewa a jiya juma'a sojoji da dakarun sa-kai, sun kai hari da manyan bindigogi a yankin Sarwah, a gundumar Ma'arib, tare da kashe jami'an sojojin Saudiyya da dama.
Daga cikin wadanda aka kashe a harin na jiya da akwai Manjo-Genar Abdurra al-shidady wanda shi ne kwamandan 'yan koren Saudiyya a Yamen.
Bugu da kari, daga cikin wadanda aka kashe da akwai Shayif al-amury da Ali al-humaisy da su ke cikin kwamandojin sojojin Yamen, yan kore.
Fiye da shekara guda kenan dai da Saudiyya ta shelanta yaki akan kasar Yamen da al'ummarta.