Martanin Duniya Kan Kisan Kiyashin Da Saudiyya Ta Tafka A Yemen
(last modified Mon, 10 Oct 2016 07:18:40 GMT )
Oct 10, 2016 07:18 UTC
  • Martanin Duniya Kan Kisan Kiyashin Da Saudiyya Ta Tafka A Yemen

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini dangae da hare-haren kisan kiyashi da Saudiyya ta kai kan al’ummar birnin Sana’a fadar mulkin kasar Yemen a ranar Asabar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 150 tare da jikkatar wasu daruruwa na daban.

A nata bangaren jamhuriyar muslunci ta Iran ta bayyana wannan kisan kiyashi  da cewa aiki ne na dabbanci wanda ya yi hannun riga da ‘yan adamtaka, wanda yake a matsayin laifin yaki da ya cancanci a hukunta masarautar Saudiyyah a kansa a gaban kotun manyan laifuka ta duniya.

Shi kuwa jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Alhuthi cewa ya yi, wannan kisan kiyashi ya kara fito da hakikanin fuskar wannan masarauta ta 'ya'yan Saud da turawan Ingila suka kafa a cikin kasar Hijaz, wadda ba ta da aiki sai haifar da fitina da da yaki da kashe-kashe a tsakanin musulmi,  tare da rarraba kawunansu, wanda a lokuta da dama tana yin amfani da kungiyoyin ta’addanci da ta kafa ne masu dauke da akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi, inda suke kashe dubban musulmi ba ji ba gani da sunan jihadi, kamar yadda kowa yake gani a Syria, Iraki, Libya, Afghanistan, Pakistan, Somalia da sauransu, amma a kasar Yemen masarautar Saudiyyah da kanta ne take aiwatar da wannan ta’addanci kan mata da kananan yara da tsoffi, tare da rusa makarantu da masallatai, asibotoci,  kasuwanni da gidajen jama’a, kuma duk hakan yana faruwa ne a kan idanun manyan kasashen duniya, wanda ma wasu daga cikinsu kamar Amurka da Birtaniya ba su boye ma duniya ba kan cewa suna taimaka ma Saudiyya wajen kaddamar da hare-hare kan al’ummar kasar Yemen.

Alhuthi ya ce wannan babban abin kunya ne wanda ya kara zubatar da martabar manyan kasashen duniya da kuma majalisar dinkin duniya, domin a cewarsa hakan ya tabbatar wa dukkanin al’ummomin duniya cewa maslahar manyan kasashe ita ce a gabansu, ba rayukan jama’a ko hakkokinsu ba, domin kuwa matukar za su kwashi mai a Saudiyya, kuma masarautar kasar za ta ci gaba da yi musu cinikin makamai, babu abin da ya dame su da adadin rayukan da za ta kashe, a Yemen ne ko a Syria ko a Iraki,  ko ma a ina ne a cikin kasashen musulmi da na larabawa.

A nata bangaren gwamnatin Rasha ta yi Allawadai da kakkausar murya kan wannan kisan kiyashi da Saudiyya ta yi wa daruruwan jama'a a birnin San'a a ranar Asabar da ta gabata, tare da tabbatar da cewa dole ne a gudanar da bincike na kasa da kasa kan wannan lamari, tare da hukunta duk wani mai hannu a cikin lamarin a gaban kotun duniya.

Ita ma a nata a bangaren majalisar dinkin duniya a ta bakin babban sakatarenta Ban Ki Moon ta bayyana cewa, dole ne a yi binciken gaggawa kan wannan danyen aiki.

A wani abu mai kama da borin kunya, ita ma gwamnatin Amurka ta bayyana cewa za ta sake yin nazari dangane da taimakon da take baiwa Saudiyya wajen kaddamar da hare-hare kan al’ummar kasar Yemen, biyo bayan kisan gillar da Saudiyya ta yi a birnin san’a a wannan  Asabar, wanda ya lakume rayukan fararen hula masu tarin yawa.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun sha alwashin ganin cewa za su bi dukkanin hanyoyi na doka har sai inda karfinsu ya kare, domin ganin an gurfanar da mahukuntan kasar Saudiyya a gaban kotun manyan laifuka ta duniya, domin hukunta su kan kisan kiyashin da suke tafkawa kan miliyoyin fararen hula a Yemen.