Sharhi: Fara Kaddamar Da Farmakin Tsarkake Mausul Daga 'Yan Ta'addan ISIS
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i12598-sharhi_fara_kaddamar_da_farmakin_tsarkake_mausul_daga_'yan_ta'addan_isis
Tun da jijjifin safiyar jiya Litinin ne gwamnatin Iraki ta sanar da fara aiwatar da shirin tsarkake Mausul daga mamayar ‘yan ta’addan takfiriyyah na ISIS, bayan kammala dukkanin shirye-shiryen da rundunar sojin kasar ke yi kan hakan.
(last modified 2018-08-22T06:59:06+00:00 )
Oct 18, 2016 02:13 UTC
  • Sharhi: Fara Kaddamar Da Farmakin Tsarkake Mausul Daga 'Yan Ta'addan ISIS

Tun da jijjifin safiyar jiya Litinin ne gwamnatin Iraki ta sanar da fara aiwatar da shirin tsarkake Mausul daga mamayar ‘yan ta’addan takfiriyyah na ISIS, bayan kammala dukkanin shirye-shiryen da rundunar sojin kasar ke yi kan hakan.

A lokacin da yake zantawa da manyan jami’an gwamnati da kuma manyan hafsoshin soji na kasar Iraki a jiya, Firayi ministan kasar Haidar Abadi ya bayyana cewa, babu gudu babu ja da baya a shirin tsarkake Mausul, kuma sojojin Iraki da rundunar hadin gwiwa ta yaki da ta’addanci gami da sojojin sa kai na al’ummar kasar ne za su gudanar da wannan gagarumin aiki.

Haka nan kuma Haidar Abadi ya gargadi Turkiya da cewa ta janye sojojinta daga yankin da ke tsakanin Mausul da Turkiya, domin kuwa ba a gayyace ta a cikin wannan aiki ba, kuma ci gaba da kasancewar sojojinta a wurin suna a matsayin abokan gaba ne.

Wasu daga cikin kasashen larabawa yankin tekun Fasha da suke da hannu kai tsaye wajen daukar nauyin ‘yan ta’addan ISIS, da suka hada da Saudiyyah, UAE gami da Qatar, sun nuna damuwa matuka kan batun tsarkake Mausul daga ‘yan ta’addan ISIS, amma ganin yadda gwamnatin Iraki ta lashi takobin kan lamarin hakan ya sanya Qatar da UAE sun yi gum da bakunansu, in ban da Saudiyya wadda ita kadai ce a halin yanzu take sukar lamarin, inda ministan harkokin wajenta Adel Jubair ya ce suna yin Allawadai da kakkausar murya kan shirin da sojojin Iraki suke yi na kwace Mausul daga hannun ISIS, inda ya ce ana shirin murkushe ‘yan sunna ne.

Wasu majiyoyin tsaro a Iraki sun tabbatar da cewa, rundunar sojin kasar tana samun gagarumin taimako daga Iran da Rasha, inda kwararru kan harkokin soji na kasar Iran suke bayar da dabaru na yaki ga sojojin na Iraki, yayin da Rasha take bayar da bayanai na asiri ga rundunar sojin na Iraki, inda ko a jiya Litinin dakarun na Iraki sun samu nasarar kwace kauyuka 11 da suke kusa da birnin Mausul, a daidai lokacin da suke ci gaba da killace garin ta kusurwoyi daban-daban, tare da kaddamar da hare-hare ta sama da kuma harba makaman atilare a kan sansanonin ‘yan ta’addan na ISIS, inda ko a daren jiya jiragen yakin Iraki sun ragargaza wasu jerin motoci guda 30 da suke dauke da mayakan ISIS da suka fice daga Mausul suka nufin iyakokin kasar Syria, inda aka halaka dukkanin 'yan ta'addan da ke cikin motocin guda 30, wadanda dukkaninsu 'yan kasashen ketare ne.

Masana kan harkokin tsaro na ganin cewa, kwace iko da Mausul daga hannun ISIS zai zama babbar nasara ga gwamnatin Iraki ta fuskar yaki da ta’addanci, kamar yadda hakan zai yi gagarumin tasiri wajen kara karya lagon kungiyar a cikin kasar Syria, inda a halin yanzu Saudiyya da Turkiya suke ta hankoron ganin sun sama ma dubban ‘yan ta’addan hanyar arcewa daga Mausul zuwa cikin kasar Syria, yayin da wasu majiyoyin sirri kuma suke tabbatar da cewa, hankoron da Saudiyya da Turkiya gami da Amurka suke yi na fitar da wasu ‘yan ta’adda daga Mausul zuwa Syria, dubara ce ta fitar da wasu manyan jami’an leken asiri na kasashen Turkiya, Saudiyya da jami’an Mossad na Isra’ila, wadanda suke aiki tare da ‘yan ta’addan na ISIS a cikin garin Mausul, kamar yadda kuma suke son yin amfani da hakan domin kara ma ‘yan ta’addan ISIS karfi a cikin Syria, musamman a yankunan Deir Zur da kuma Tadmur.

To koma dai yaya lamarin yake, ga dukkanin alamu dai karshen ‘yan ta’addan ISIS ya karato a babbar tungarsu da ke Iraki, bayan tsarkake Ramadi, Falluja da kuma Tikrit, duk kuwa da cewa ‘yan siyasa a Amurka, musamman ma ‘yan jam’iyyar Democrat, da ‘yar takararsu Hillary Clinton, suna son su yi amfani da wannan damar a matsayin wani makamain yakin neman zabe, inda suke nuna ma duniya cewa su ne kan gaba wajen taimakon Iraki domin kwato Mausul daga ISIS, duk da cewa abin da yake wakana a zahiri na yunkurin da sojojin Iraki da sojin sa kai na al’ummar kasar ke yi domin tsarkake Mausul, na karyata abin da ‘yan siyasar na Amurka ke ikirari.