Yemen : An Yi zanga zangar Kyammar Wakilin MDD
Magoya bayan 'yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsis a Yemen sun gudanar da wata zanga zanga yau Asabar domin nuna adawa da tsarin samun lafiya da wakiln musamen na MDD, Ismaïl Ould Cheikh Ahmed ya gabatar.
Masu zanga-zanga dai da suka taru a harabar Otel din da wakilin na MDD ya sauka na raira taken '' ba ma so'' kuma ba zamu taba bada kai ba''.
Daya daga cikin masu zanga zanga ya shidawa kanfanin dilancin labaren AFP cewa matakin da MDD ta dauka abun kunya ne tare da kira ga wakilin na MDD daya ryfe bakinsa ya kuma fice daga kasar.
A ranar Alhamis data gabata ne wakilin musamen na MDD kan rikicin kasar ta Yemen, ya isa birnin Sanaa a karo na biyu cikin mako guda inda ya gabatar da wani shirin samar da zamen lafiya na MDD daya tanadi wata yerjejeniyar soji inda 'yan Houtsis zasu mika mayan makaman yakinsu sanan su fice daga yankunan da suke rikeda tun cikin shekara 2014.
Haka zalika shirin ya kunshi wani bangare na siyasa inda za'a nada mataimakin shugaban kasa da kuma kafa gwamnatin hadin kan kasa.
Tun dai bayan da kawacen da Saudiyya ke jagoranta ya soma kai farmaki a kasar ta Yemen a watan Maris na shekara 2015, kimanin mutane 7,000 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 35,000 suka raunana a cewar alkalumen MDD.