Dakarun Kasar Yamen Sun Kaddamar Da Hari Kan Sojojin Kasar Saudiyya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i13825-dakarun_kasar_yamen_sun_kaddamar_da_hari_kan_sojojin_kasar_saudiyya
Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun kaddamar da wani harin daukan fansa kan tawagar sojojin masarautar Saudiyya a kudancin kasar ta Saudiyya, inda suka kashe da dama daga cikinsu.
(last modified 2018-08-22T06:59:14+00:00 )
Nov 13, 2016 13:45 UTC
  • Dakarun Kasar Yamen Sun Kaddamar Da Hari Kan Sojojin Kasar Saudiyya

Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun kaddamar da wani harin daukan fansa kan tawagar sojojin masarautar Saudiyya a kudancin kasar ta Saudiyya, inda suka kashe da dama daga cikinsu.

Kafar watsa labaran kasar Yamen ta bayyana cewa: Sojojin Yamen da hadin gwiwar dakarun sa- kai na kasar sun kadamar da wani harin daukan fansa kan tawagar sojojin Saudiyya a yankin Jizan da ke kudancin kasar Saudiyya a yau Lahadi, inda suka yi nasarar halaka adadi da dama na sojojin.

Har ila yau sojojin kasar Yamen sun kai hari da makamai masu linzami kan sansanin sojojin mamayar Saudiyya da ke lardin Ma'arib, inda harin ya yi sanadiyyar mutuwa tare da jikkatan sojoji masu yawa.

A gefe guda kuma jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan yankin garin Masurah da ke gundumar Sarwah a lardin Ma'arib a yau Lahadi, inda suka janyo hasarar dukiya ga al'ummar yankin.