Saudiyya Na ci gaba da kai wa Kasar Yamen hari
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i13858-saudiyya_na_ci_gaba_da_kai_wa_kasar_yamen_hari
Saudiyya ta sake kashe mutane a yau litinin A kasar Yamen.
(last modified 2018-08-22T06:59:14+00:00 )
Nov 14, 2016 08:29 UTC
  • Saudiyya Na ci gaba da kai wa Kasar Yamen hari

Saudiyya ta sake kashe mutane a yau litinin A kasar Yamen.

A harin da jiragen yakin Saudiyya su ka kai a yankuna daban-daban na kasar Yamen a yau litinin sun kashe mutane da dama.

 Jiragen na Saudiyya sun harba bama-bamai masu kwafsa a arewa maso yamacin birnin Sanaa.

A  gefe daya sojojin kasar Yamen, sun kai wasu hare-haren a kan iyakokin kasar Saudiyya inda su ka lalata sansanoni da dama.

Watanni 20 kenan da Saudiyyar ta fara kai hari akan kasar Yamen, wanda kawo ya zuwa yanzu ta kashe fiye da 10,000.

Manufar Saudiyyar dai ita ce mayar da Abdul-Hadi, akan gwamnatin kasar bayan da wa'adinsa ya kare,